‘Yan bindiga sun harbe wani jami’in ɗan sanda a Oka-Akoko da ke Ƙaramar Hukumar Akoko ta Yamma a Jihar Ondo.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo DSP
Funmilayo Odunlami ta bayyana haka yayin wata hira da gidan
talabijin ta Channels.
Mazauna yankin dai sun shiga ruɗani sakamakon faruwar
lamarin, bayan maharan sun isa a kan Babura su ka harbe ɗan
sandan sannan su ka arce.
Funmilayo Odunlami ta ƙara da cewa, tuni sun ƙaddamar da
bincike domin gano waɗanda su ka aikata kisan.
Wata majiya ta ce tuni an kai gawar jami’in, wanda ba a
bayyana sunan sa ba dakin ajiye gawa a wani asibiti da ke kusa.

