Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yadda Zaman Kotun Kalubalantar Nasarar Bola Tinubu Ya Kasance A Abuja

An shiga rana ta biyu ta ci-gaba a sauraren kararrakin da su ka
shafi zaɓen shugaban kasa na shekara ta 2023.

Kotun sauraren kararrakin zaben da ke zama a Abuja, ta saurari lauyoyi daga ɓangaren jam’iyyar PDP da ɗan takarar ta Atiku Abubakar da kuma jam’iyyar APM.

Kotun, wadda ta zauna a karkashin alkalai biyar da mai shari’a Haruna Tsammani ke jagoran ta, ta fara ne da sauraren karar jam’iyyar APM ta shigar a zaman share fagen sauraren karrarakin da ta yi.

Jam’iyyar APM ta shaida wa kotun cewa, ta bada dukkan bayanan da ake bukata da kuma amsoshi a takardar bayanan share-fagen saurarrn karrarakin.

Yayin da lauyoyin wadanda ta ke kara wato hukumar zaɓe ta kasa da jam’iyyar APC dan takarar ta da mataimakin sa da Ibrahim Kabiru Masari su ma sun ce sun maida martani a kan tambayoyin da su ka shafi karar.

Sai dai lauyan Bola Tinubu ya shaidawa kotun cewa, ya shigar da wata bukata da ke neman a yi watsi da karar da jam’iyyar APM ta shigar saboda rashin makama.

Exit mobile version