Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kotun Koli Ta Dage Sauraren Karar Peter Obi Zuwa Ranar Laraba

Kotun sauraren kararralkin zaɓen shugaban kasa, ta dage sauraren karar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi ya shigar zuwa ranar Laraba 10 ga watan Mayu na shekara ta 2023. Haka kuma, Kotun ta ɗage zaman ta zuwa ranar Talata 9 ga watan Mayu domin sauraren ƙorafin jam’iyyar PDP da ɗan takarar ta Atiku Abubakar da kuma jam’iyyar APM. Idan dai ba a manta ba, Kotun ta fara sauraren kararrakin da ‘yan takarar shugaban kasa su ka shigar ne a ranar Litinin din nan a Abuja.
Rahotanni sun ce, shugaban kotun Mai Shari’a Haruna Tsammani ya yi watsi da karar da jam’iyyar AA ta shigar da nufin kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu. Wata Majiya ta ce, Kotun ta yi ta yi watsi da karar ne bayan mai shigar da karar Lauya Oba Maduabuchi ya janye da kan sa.

Exit mobile version