Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

 ‘Yadda Mu Ka Ƙwato Naira Biliyan 454 Daga Hannun Ɓarayin Kuɗaɗen Talakawa – ICPC

Hukumar yaki da ayyukan almundahana ICPC, ta ce a cikin shekaru huɗu ta ƙwato kuɗaɗe da kadarori na kimanin Naira biliyan 454 daga hannun manyan ɓarayin gwamnati.

Mataimakin Daraktan Tsare-tsare da, Bincike da Ƙididdiga na hukumar Jude Okoye ya bayyana haka, yayin da ya ke gabatar da Kundin Nasarorin da hukumar ta samu daga shekara ta 2019 zuwa watan Maris na shekara ta 2023.

Jude Okoye ya yi gabatarwar ne, a ranar da aka rufe taron kwanaki biyu da hukumar ICPC ta shirya wa ‘yan jarida masu ɗauko labarai a hukumar.

Da hukumar  ICPC ta ce ta Ƙwato daga Hannun Ɓarayin Gwamnati sun hada da Naira biliyan 257, waɗanda ta toshe ƙofofin da Ma’aikatu da Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati su ka nemi karkatar da su, sai kuma Naira biliyan 3 da miliyan 540 na haraji da ta ƙwato.

Sauran sun hada da manyan fulotai da maka-makan gidaje da kantina da motocin alfarma da kuɗaɗe a asusun bankuna, da kuɗaɗen hayar da aka karɓa daga gidajen da gwamnati ta ƙwace ta bada haya, da kadarori da gwala-gwalai na kimanin Naira Biliyan 25 da miliyan 36.

Exit mobile version