Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Wa;adin Shekara 6: Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Kudirin Da Aka Gabatar

Nigeria House of Representatives REPS

Nigeria House of Representatives REPS

Majalisar wakilan Najeriya ta yi watsi da kudirin dokar da ke neman bayar da damar wa’adin shekara shida akan mulki ga shugaban kasa da gwamnanoni.

Kudirin dokar wanda ‘yan majalisu 34 suka gabatar da shi, ya bukaci da a gudanar da zabukan gwamnoni da na shugaban kasa a rana guda.

Kudirin an sake gabatar da shi ne domin shiga karatu na biyu, wanda dan majalisar Imo Ugochinyere, ya gabatar a zauren majalisar.

Lokacin da shugaban majalisar, Abbas Tajuddeen ya gabatar da sunan kudirin, ‘yan majalisar sun yi ta ihun “ba sa so” wanda hakan ya nuna bai karbu ba.

Daga bisani shugaban majalisar ya bayyana cewa, an yi watsi da wannan kudiri da ya gaza samun goyon bayan mafiya rinjaye na ‘yan majalisar, wanda ya tsallake karatu na farko.

Exit mobile version