Tsohon babban hafsan sojin ruwa a Najeriya, ya kai ƙara gaban kotu domin hana tsohuwar mai ɗakin sa Diezani Alison Madueke yin amfani da sunan sa.
Madueke ya buƙaci kotu ta ba tsohuwar ministan man fetur ɗin umarnin ta koma yin amfani da sunan mahaifin ta Agama kasancewar auren su ya riga ya mutu.
Ya kuma wallafa a jaridun Najeriya da waɗanda ke Burtaniya inda yake neman tsohuwar matar tasa ta daina amfani da sunan sa.
A takardar ƙorafin, Madueke ya ce ci gaba da amfani da sunan sa haɗari ne ta fuskar shari’a da kuma sha’anin kuɗi musamman yadda take fuskantar shari’a.
Madueke ya ƙara da cewa tsohuwar matar ta sa na kunyatar da shi ganin yadda take ci gaba da bayyana kanta a matsayin mai ɗakin sa duk da cewa sun rabu.

