Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsohon Gwamna, Masu Bankuna Da Wasu Kwararru Da Ke Sa Ran Gaje Kujerar Emefiele

Rahotanni na cewa, yanzu haka Shugaba Bola Tinubu da
hadiman sa su na fafutukar neman wanda zai gaji kujerar
gwamnan babban bankin CBN Godwin Emefiele.

Wata majiya ta ce, Shugaba Tinubu da mukarraban sa dai, su na duba yiyuwar samun mutane masu kwarewa domin a ba su mukamai daban-daban a sabuwar gwamnatin.

Majiyar ta ce, kujarar shugabancin CBN ta na bukatar natsuwa domin tabbatar da wanda zai gaje ta ya kawo sauyi musamman duba da yadda tattalin arzikin Nijeriya ya lalace.

Daga cikin wadanda ake sa ran za su gaji kujerar akwai Fola Adeola, da Bode Agusto da Oluyemi Cardoso da kuma Olawale Edun.

Exit mobile version