Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsohon Ɗan Wasan Kamaru Landry Nguemo Ya Mutu

d850d400 1508 4c7f 8d6f 8ec17c44848f

d850d400 1508 4c7f 8d6f 8ec17c44848f

Tsohon ɗan wasan tawagar Kamaru Landry Nguemo ya mutu bayan wani mummunan hatsarin mota a Kamaru.

ɗan wasan ya taka leda a ƙungiyoyin Parkhead da Nancy da kuma wasu kungiyoyin ƙasashen Turkiyya da kuma Celtic.

Hukumomin ƙwallon ƙafar Kamaru sun tabatar da mutuwar tsohon ɗan wasan ne mai shekara 38

a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da shi tsakanin Yaounde da Bafousam.

FECAFOOT ta ce za ta ci gaba da tuna Nguemo, wanda ya taka mata leda tsakanin shekarar 2006 zuwa 2014.

Haɗuran ababen hawa dai ya zama ruwan dare a titunan Kamaru,

inda ya zama ɗaya daga cikin hanyoyi da ke hallaka al’ummar ƙasar da ke tsakiyar Afirka.

Exit mobile version