Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Tawagar Gwamnonin Arewa Ta Dira Jamhuriyar Nijar

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Tawagar Gwamnonin Arewa Ta Dira Jamhuriyar Nijar

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Tawagar Gwamnonin Arewa Ta Dira Jamhuriyar Nijar

A kokarin sa na kawo karshen ayyukan ta’addanci da su ka addabi sassan jihar Katsina ba dare ba rana, gwamnan jihar Aminu Bello Masari, ya fara tattaunawa da takwaran sa na jihar Maradi ta jamhuriyar Nijar Zakari Umaru.

Karanta Wannan: Rantsar Da Buhari: Gwamna Masari Ya Soke Bikin Ranar 29 Ga Watan Mayu A Katsina

Jihar Maradi dai ta yi iyaka da Nijeriya ta jihar Katsina da jihohin Sokoto da Kebbi da kuma Zamfara.

Tawagar da masari ya nada a karkashin sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustafa Mohammed Inuwa, ta isa jamhuriyar Nijar tare da wasu gwamnoni da su ka hada da Bello Matawalle na jihar Zamfara, da Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, da kuma Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Gwamnonin sun tattauna a kan magance ayyukan ‘yan bindiga a tsakanin jihohin arewacin Nijeriya da makwaftan garuruwan jamhuriyar Nijar.

Ziyarar da tawagar ta kai dai ta na zuwa ne, a daidai lokacin da gwamna Masari ya fara tattaunawa domin yin sulhu da ‘yan bindigar da su ka hana kananan hukumomi takwas daga cikin 34 na jihar Katsina zaman lafiya.

Exit mobile version