Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tinubu Zai Sanar Da Sabuwar Ranar Kidayar Jama’a Da Gidaje – NPC

Shugaban hukumar kidaya ta kasa NPC, Nasir Kwarra, ya ce
Shugaba Tinubu da kan sa ne zai sanar da sabuwar ranar da za
a gudanar da aikin kidayar jama’a da gidaje da aka dage a
watan Afrilun da ya gabata.

Nasir Kwarra ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, bayan tawagar sa ta yi wa shugaban kasa cikakken bayani.

Ya ce hukumar ta mika rahoton ta ga shugaban kasa, wanda ake sa ran zai yi nazari tare da yanke shawarar lokacin da za a gudanar da aikin kidayar a fadin Nijeriya.

Nasir Kwarra ya kuma yi nuni da cewa, akwai yuwuwar hukumar ta kara bijiro da bukatun karin kudaden gudanarwa, ya na mai cewa idan aka dade ana jinkirin aikin zai iya kara yin tasiri a kan kudin gudanar da aikin.

Exit mobile version