Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tinubu Ya Shirya Biyan Bashin Dala Miliyan 500 Na Eurobond A Watan Yulin 2023

Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyar cika alkawarin da ta
dauka na biyan basussukan da ake bin Nijeriya, inda ta shirya
biyan bashin dala miliyan 500 a watan Yuli na shekara ta
2023.

Wannan matakin ya nuna yadda gwamnatin tarayya ta maida hankali a kan alhakin kudi, da kuma jajircewar ta wajen ci- gaba da tabbatar da amincin Nijeriya a kasuwannin hada- hadar kudi ta duniya.

Ta hanyar cimma wannan yunkuri na biyan basussukan, Nijeriya ta na da burin bunkasa kwarin gwiwar masu zuba jari, da kuma karfafa sunan ta a matsayin amintacciyar kasa mai karba da kuma biyan bashi a fagen kasa da kasa.

Rahotanni daga ofishin kula da basussuka na kasa na nuni da cewa, Nijeriya ta na shirin biyan dala miliyan 500 a watan Yuli na shekara ta 2023, wanda ya yi daidai da sharuddan lamunin.

Haka kuma, Rahotannin baya-bayan nan na nuni da cewa, basusukan da ake bin Nijeriya sun haura Naira Tiriliyan 82, biyo bayan hadewar Naira tiriliyan 73.

Exit mobile version