Hukumar kula da basussuka ta kasa DMO, ta ce bashin kudin da ake bin Nijeriya ya yi tashin gwauron zabo, daga naira tiriliyan 3 da biliyan 32 zuwa naira tiriliyan 25 da biliyan 7 a cikin shekara daya, a cewar
Ta ce ana bin gwamnatin tarayya bashin naira tiriliyan 20 da biliyan 42 a ranar 30 ga watan Yuni na shekara ta 2019, inda jihohi 36 da kuma gwamnatin tarayya ake bin su jimillar kudi naira tiriliyan 5 da biliyan 28.
Jimillar bashin ya hada da naira tiriliyan 8 da biliyan 32, wanda ya ke daidai da dala biliyan 27 da miliyan 16 bashin waje, da kuma naira tiriliyan 17 da biliyan 38 bashin cikin gida kamar yadda hukumar ta sanar.
Bashin Nijeriya ya tsaya a naira tiriliyan 22 da biliyan 38 ne a watan Yuni na shekara 2018, inda ya haura zuwa naira tiriliyan 24 da biliyan 39 a watan Disamba na shekara ta 2018, kafin dagawar sa zuwa naira tiriliyan 24 da biliyan 95 a watan Maris na shekara ta 2019.
A watan da ya gabata ne, kwamitin dokokin kudi na babban bankin Nijeriya, ya ce hauhawar bashin Nijeriya na daya daga cikin abubuwan da ke dakile da ci-gaban ta.