Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Takaddama: PDP Ta Zargi Gwamnatin Tarayya Da Sace Naira Tiriliyan 14

Jam’iyyar PDP ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da batar da kudi naira tiriliyan 14 cikin shekaru 4 na farkon mulkin sa.

Wata sanarwa da sakataren yada labaran Jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya fitar ta yi zargin cewa, tsoron bankado badakalar kudaden ne ya tilastawa shugaban kasa neman sake ci gaba da wanzuwa a mulki zuwa shekaru 4.

Sanarwar ta ce kudaden da gwamnatin shugaban kasa Buhari ta wawure sun hada da Naira Tiriliyan 9 daga ma’aikatar man fetur da ma wasu triliyan 1 da biliyan dari 4 na tallafin man fetur da gwamnatin ta yi ikirarin cirewa, da  kuma naira Tiriliyan 1 da biliyan dari daya na danyen man fetur da gwamnatin ta sayarwa wasu kamfanoni marasa rijista.

Ta ci gaba da cewa akwai naira biliyan 33 da aka wawure daga cikin kudin da aka warewa hukumar bayar da agajin gaugawa  ta NEMA ka na da wasu naira biliyan 18 wanda wani bangare ne na biliyan 48 da majalisar zartaswa ta amince da warewa domin kula da ‘yan gudun hijira a jihohin Borno Yobe da Adamawa.

Ologbondiyan, ya yi ikirarin cewa adadin kudin da Najeriya ta ciwo bashi shi ne mafi muni a tarihi, inda yanzu haka ake bin gwamnati bashin Naira tiriliyan 24 da biliyan dari 3 da tara.

Exit mobile version