Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tada Zaune Tsaye: Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Ta Kama ‘Yan Shi’a A Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama mabiya addinin Shi’a akalla 12 bisa laifin yin zanga-zanga ba bisa ka’ida ba, tare da yin wasu abubuwa da ka iya haddasa tashin-tashina a jihar.

Jami’in yada labarai na rundunar Yakubu Sabo, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna.

Ya ce masu zanga-zangar sun saba dokar da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa na hana duk wata zanga-zanga dake da nau’in tada hatsaniya, da kuma aka yi ta ba bisa ka’ida ba.

A cewar Sabo kamen ya auku ne da misalign karfe 2 da rabi na ranar Juma’ar da ta gabata a cikin garin Kaduna, daidai lokacin da jama’a ke hada-hadarsu.

Ya ce a daidai lokacin da jami’an ‘yan sanda suka je domin tarwatsa masu zanga-zangar sai ‘yan shi’an suka fara jifa da wasu abubuwa da ka iya jiwa jami’an ciwo.

Sabo ya ce tun a baya gwamnatin jihar Kaduna ta haramta aikace-aikacen kungiyar, adon haka ya zama wajibi jami’an ‘yan sanda su tabbatar da bin wannan doka.

mnatin jihar Kaduna ta kafa na hana duk wata zanga-zanga dake da nau’in tada hatsaniya, da kuma aka yi ta ba bisa ka’ida ba.

A cewar Sabo kamen ya auku ne da misalign karfe 2 da rabi na ranar Juma’ar da ta gabata a cikin garin Kaduna, daidai lokacin da jama’a ke hada-hadarsu.

Ya ce a daidai lokacin da jami’an ‘yan sanda suka je domin tarwatsa masu zanga-zangar sai ‘yan shi’an suka fara jifa da wasu abubuwa da ka iya jiwa jami’an ciwo.

Sabo ya ce tun a baya gwamnatin jihar Kaduna ta haramta aikace-aikacen kungiyar, adon haka ya zama wajibi jami’an ‘yan sanda su tabbatar da bin wannan doka.

Exit mobile version