Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sufuri: Gwamnatin Buhari Ta Bada Izinin Gina Layin Dogo Daga Ibadan Zuwa Kano

Rotimi Amaechi, Ministan sufuri

Rotimi Amaechi, Ministan sufuri

Gwamnatin tarayya ta bada izinin gina layin dogo irin na zamani daga Ibadan zuwa Kano a kan kudi dala miliyan dubu 5 da miliyan dari 3.

Ministan sufuri Rotimi Amaechi, ya tabbatar da aikin a lokacin  da ya ke bayyana kudirin gwamnatin tarayya na inganta bangaren sufuri a Nijeriya. Rotimi Amaechi, ya ce  bayan wannan muhimmin aiki, a kwai batun fara aikin gina layin dogon daga garin Fatakwal zuwa Warri, domin inganta harkokin kasuwanci a Nijeriya.

Exit mobile version