Home Labaru Sufuri: Gwamnatin Buhari Ta Bada Izinin Gina Layin Dogo Daga Ibadan...

Sufuri: Gwamnatin Buhari Ta Bada Izinin Gina Layin Dogo Daga Ibadan Zuwa Kano

331
0
Rotimi Amaechi, Ministan sufuri
Rotimi Amaechi, Ministan sufuri

Gwamnatin tarayya ta bada izinin gina layin dogo irin na zamani daga Ibadan zuwa Kano a kan kudi dala miliyan dubu 5 da miliyan dari 3.

Ministan sufuri Rotimi Amaechi, ya tabbatar da aikin a lokacin  da ya ke bayyana kudirin gwamnatin tarayya na inganta bangaren sufuri a Nijeriya. Rotimi Amaechi, ya ce  bayan wannan muhimmin aiki, a kwai batun fara aikin gina layin dogon daga garin Fatakwal zuwa Warri, domin inganta harkokin kasuwanci a Nijeriya.