Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sokoto: ‘Yan Takarar Gwamna ‘Yan Majalisa Da Mabiya 3,000 Na APC Sun Koma PDP

Jam’iyyar APC ta rasa magoya baya kimanin dubu 3 da ‘yan takarar kujerar gwamna biyu da wani dan takarar majalisar wakilai bayan sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a jihar Sokoto.

Da ya ke jawabi a wajen bikin sauya shekar, shugaban masu sauya shekar da wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Illela da Gwadabawa a majalisar wakilai Abdullahi Balarabe Salame, ya ce sun yanke shawarar yin haka ne a lokaci guda.

Abdullahi Salame, wanda tsohon dan takarar kujerar gwamna ne a karkashin jam’iyyar APC, ya janye daga takarar ne ana saura lokaci kalilan kafin a fara zaben fidda gwanin jam’iyyar APC a jihar Sokoto.

Gwamnan jihar Sakoto Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana yadda ya shiga cikin farin ciki da tarbar wandanda su ka sauya shekar zuwa jam’iyyar PDP, ya na mai cewa tuni APC ta na neman agaji jiran mutuwa kawai ta ke yi.

Exit mobile version