Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Siyasar Zamfara: Za A Gudanar Da Zabubbukan Kananan Hukumomi A Mako Mai Zuwa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta Kasa, INEC

Hukumar zabe ta jihar Zamfara ZASIEC, ta sanar da 27 ga watan Afrilu na shekara ta 2019 a matsayin ranar da za ta gudanar da zabubbukan kananan hukumomi a jihar Zamfara.

Shugaban hukumar Alhaji Garba Muhammad ya bayyana haka a garin Gusau, yayin wata ganawa da ya yi da masu ruwa da tsaki a siyasar jihar.

Tun a ranar 2 ga watan Janairu na shekara ta 2019 ne wa’adin shugabannin kananan hukumomi da na Kansilolin jihar ya kare, amma majalisar dokoki ta jihar ta tsawaita masu wa’adin zuwa ranar 2 ga watan Mayu na shekara ta 2019.

Shugaban hukumar ya bada tabbacin cewa, sun samu dukkan gudunmuwar kudi da su ke bukata na gudanar da zaben daga gwamnatin jihar, don haka za su fara wayar da kawunan jama’a game da muhimmancin zaben ta hanyar amfani da kafafen yada labaru da tarurruka.

A karshe ya bayyana wa mahalarta taron cewa, yanzu haka sun kammala aikin horar da jami’an zabe, tare da tura su rumfunan zaben da za su gudanar da aikin su a kananan hukumomin jihar, sai dai jam’iyyar PDP ta kaurace wa taron kwata-kwata.

Exit mobile version