Wata kungiyar Shugabannin Jam’iyyar NNPP, ta zargi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da yi wa Jam’iyya zagon-kasa.
Shugaban kungiyar Kwamred Sunday Oginni ya bayyana haka, inda ya ce su na zargin Rabi’u Musa Kwankwaso da yi wa jam’iyyar NNPP zagon kasa.
Daga cikin abubuwan da su ke zargin Kwankwaso da aikatawa akwai alakar sa da shugaba Bola Ahmed Tinubu. Shugabannin Kungiyar na jihohi, sun kuma bukaci Rabi’u Musa Kwankwaso da ya rubuta takardar murabus daga Jam’iyyar ba tare da bata lokaci ba.