Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shugaban Kasa Buhari Ya Mika Turar Takarar Shuugaban Kasa Ga Bola Tinubu

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya miƙa turar jam’iyyar APC ga Bola Ahmed Tinubu a wajen babban taron tsaida ɗan takarar shugaban ƙasa a Abuja.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa a kan harkokin kafafen sada zumunta Buhari Sallau ya bayyana haka a shafin sa na Twitter.

Shugaba Buhari tare da shugaban jam’iyyar na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu, da matar Osinbajo, ya damƙa tutar ne yayin rufe taron da ya tabbatar da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Ya ce shugaban Buhari ya mika wa Tinubu tutar ne a gaban shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu da uwargidan Tinubu Oluremi Tinubu.

Wakilan jam’iyyar APC dai sun zabi Bola Tinubu a matsayin wanda zai rike tutar jam’iyya zuwa ga nasara a zaben shekara ta 2023.

Exit mobile version