Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shugaban China Xi Jinping Ya Rubuto Wa Shugaba Buhari Wasika

Shugaban kasar China Xi Jinping, ya rubuto wa shugaba Muhammadu Buhari wasika, inda ya ce China ta na da burin ganin kawancen da ke tsakanin kasashen biyu ya kai wani babban mataki.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar dauke da sa hannun Femi Adesina, ta ce shugaba Xi Jinping ya kwatanta Nijeriya a matsayin muhimmiyar kasa a huldar da China ke yi da nahiyar Afirka.

Ya ce dangantakar da ke tsakanin China da Nijeriya, ita ce ginshikin kawancen China da nahiyar Afirka.

A cikin wasikar da ya aiko wa shugaba Buhari, Shugaba Xi Jinping ya ce kulla huldar diflomasiyya da kasashen su ka yi ta cika shekaru 50.

Xi Jinping dai ya aiko wa shugaba Buhari wasikar ce a matsayin amsar wasikar da Buhari ya aika ma shi, ta taya kasar China murnar cika shekaru 72 da kafa Jamhuriyar China.

Exit mobile version