Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shugaba Tinubu Ya Na Da Sauran Lokaci Game Da Nadin Ministoci

Babban Mai Taimaka wa Shugaban kasa akan hulda da
manema labarai Abdulaziz Abdulaziz, ya ce babban abin da
Shugaba Tinubu ya sa a gaba tun bayan dawowar sa daga
kasar Guinea-Bissau shi ne tattara sunayen ministocin da zai
nada.

Abdulaziz Abdulaziz, ya ce Tinubu ya na kara tantance sunayen ne kafin ya ya aike wa majalisar dattawa domin neman yardarm ta.

Ya ce tantance sunayen ne ya janyo tsaiko, saboda Nijeriya kasa ce mai yawan jama’a kuma a ciki mutane 42 kacal za a zabo, don haka idan ba a natsu ba sai a yi kitso da kwarkwata.

Abdulaziz ya kara da cewa, akwai kuma bincike na tsaro domin tabbatar da kyan hali da kuma tabbatar da cewa mutum ba ya da wata matsala, wanda bincike ne jami’an tsaro ke gudanarwa.

Exit mobile version