Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Damfara Na Karbar Kudin ‘Wasu Masu Son Zama Ministoci – Kabir Masari

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa Ibrahim
Kabir Masari, ya ce wasu ‘yan damfarar siyasa su na karbar
kudi daga hannun wasu da sunan za su sa shugaba Tinubu ya
nada su Ministoci.

Ibrahim Masari, ya ce akwai wadanda ke karbar takardun kwarewar aikin mutane, tare da yaudarar cewa za su kai hukumar DSS da EFCC domin tantancewar samun mukamai.

Ya ce su na da ingantaccen rahoto cewa akwai wadanda ke karbar kudaden mutane da takardun su cewa shugaban kasa ya ce su je su tantance mutane ko su zakulo mutanen da za a nada mukamai, ya na mai cewa wannan magana ba gaskiya ba ce.

Da ya ke magana kan wani jerin sunayen mutane da a ka fito da shi da ke nuna wadanda aka nada ministoci, Masari ya ce masu gaugawa ne su ka aikata haka da kuma masu mara masu baya, domin a cewar sa, Tinubu zai bayyana wa duniya jerin sunayen ministocin ko kuma za a ji jawabi daga bakin sa.

Exit mobile version