Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shugaba Buhari Ya Ba Tinubu Da Shettima Lambobin Girmamawa

Shugaban kasa Muhammmadu Buhari, ya karrama Bola
Ahmed Tinubu da lambar girma mafi daraja ta GCFR, yayin
da ba mataimakin shugaban kasa mai jiran-gado Kashim
Shettima lambar girmama ta GCON.

Buhari ya ba zababbun shugabannin lambobin ne tare da takardun mulki a Abuja a shirye-shiryen da ake yi na rantsar da sabuwar gwamnati.

Za a dai rantsar da sabuwar gwamnatin ne bayan zaben shekara ta 2023, wanda dan takarar jam’iyyar APC Bola Tinubu ya yi nasara.

Sai dai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour sun a kalubalantar nasarar Tinubu a kotu.

Exit mobile version