Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sa 19 ga watan Junairu na shekara ta 2022 a matsayin ranar sauraren karar da Shiek Ibrahim El-Zakzaky da matar sa su ka shigar a kan hukumar tsaro ta DSS da kuma Atoni Janar na tarayya.
Mai shari’a Inyang Ekwo, ya zabi ranar ne domin a ba hukumar DSS da ministan shari’a damar maida martani a kan zargin take hakkin dan Adam da aka shigar a kan su.
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matar sa dai sun bukaci Gwamnati ta biya su kudin asarar da aka ja masu sakamakon ci-gaba da rike Fasfon sun a shiga kasa da kasa.
Sun ce yayin da su ka yi niyyar sabuntan Fasfon su a ofishin hukumar shige da fice an bayyana masu cewa hukumar DSS ta hanadon haka sun bukaci kotu ta wajabta wa gwamnati ta biya su naira Biliyan 4 a kan take hakkin su na dan Adam da kuma ‘yanci, duk da cewa kotu ta wanke su a ranar 28 ga Yuli na shekara ta 2021.