Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Tattauna Da Tinubu

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, ya
tattauna da zababben Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta
wayar tarho.

Wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya fitar a shafin yanar gizo, ta ce tattaunawar da su ka yi ta karkata ne a kan yadda Amurka da Nijeriya za su kara yaukaka dangantakar su.

Ta ce Sakataren harkokin wajen Amurka ya tattauna da Tinubu ne don ya kara nuna shirin Amurka na ci-gaba da karfafa dangantakar ta da gwamnatin Nijeriya mai jiran gado.

Sanarwar ta kara da cewa, an gina kawancen kasashen biyu ne a kan wasu muradu da su ke girmamawa, da kuma kyakkyawar alakar da ke tsakanin al’ummar kasashen biyu, sannan akwai bukatar alakar ta dore a karkashin Bola Ahmed Tinubu.

Blinken da Tinubu, sun kuma tattauna a kan muhimmancin shugabancin da zai dama da daukacin ‘yan Nijeriya, da hadin kai a fannin tsaro da samar da sauye-sauye domin tallafa wa fannin tattalin arziki.

Exit mobile version