Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya ajiye mukamin
sa na Sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Yamma a
majalisar dattawa.
Haka kuma, dan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta Arewa
Sanata Abubakar Kyari shi ma ya sanar da ajiye na shi
mukamin.
Matakin ‘yan majalisun biyu dai ya biyo bayan zaben su da aka
yi na shugabancin jam’iyyar APC.
‘Yan majalisar sun sanar da ajiye mukaman su ne a cikin wasu
wasiku daban-daban da su ka aike wa majalisar dattawa,
wadanda shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ya karanta a
zauren majalisar.
A baya dai Sanata Abdullahi Adamu ne ya jagoranci kwamitin
kula da harkokin noma da raya karkara na majalisar dattawa,
yayin da Sanata Kyari ke shugabantar kwamitin kula da birnin
tarayya Abuja.