Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sabon Hakimin Bichi: Sarki Sanusi Ii Zai Sake Ayyana Ranar Naɗi

sanusi 4

sanusi 4

Sarki Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa za a sake sanya ranar naɗa ‘Wamban Kano’ a matsayin Hakimin Bichi a Masarautar Kano.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar tawagar shugabanni masu rike mukamai na masarautar da Malaman addini a fadarsa da ke Kano.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata ne, jami’an tsaro suka tare fadar Sarkin Kano tare da hana Sarki Sanusi II tafiya don gudanar da bikin nada Munir Sunusi a matsayin Hakimin Bichi.

Tawagar wacce shugaban karamar hukumar Bichi, Hamza Sule ya jagoranta, ta je fadar ne domin jaddada mubaya’ar al’ummar Bichi ga masarautar.

Exit mobile version