Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Remi Tinubu Ta Sanya Wa Babban Dakin Taron Cibiyar Mata Ta Abuja Sunan Maryam Abacha

Uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu, ta sauya sunan
babban dakin taro na ‘Maryam Babangida zuwa sunan
Maryam Abacha.

Zauren, wanda a da ake kira da ‘African Peace Mission Hall’, a Turance, uwargidan shugaban kasar ce ta kaddamar da shi kuma aka canza ma shi suna zuwa Maryam Abacha, saboda irin gudummawar da ta bada wajen samar da zaman lafiya a nahiyar Afrika.

Sanata Oluremi Tinubu, ta ce taron muhimmi ne a kokarin hadin gwiwa wajen karfafa alaka tare da bunkasa ci-gaban da aka samu wajen samun hadin kai da dawwamammiyar dangantaka a tsakanin mata.

Haka kuma, ta bayyana Maryam Abacha a matsayin mace mai hazaka kuma jajirtacciya wajen ci-gaban nahiyar Afrika baki daya.

A nata bangaren, Dakta Maryam Abacha ta yi wa Nijeriya da gwamnatin shugaba Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima addu’a a kan Allah ya ba su ikon cimma nasara.

Exit mobile version