Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Mata Sun Cancanci Samun Karin Mukamai A Gwamnati — Remi Tinubu

Uwargidan Shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu ta ce bai kamata a yi watsi da mata ba, maimakon haka ya kamata a ba su karin damarmaki a bangaren shugabanci da mulki domin a ba su dama wajen kyautata ci-gaban Nijeriya.

Sanata Oluremi ta bayyana haka ne a Abuja, yayin kaddamar da wani littafi da matar shugaban hafson sojojin Nijeriya Salamatu Yahaya ta rubuta.

Oluremi Tinubu wadda ta samu wakilcin Sanata Nora Daduut, ta ce akwai bukatar a sake nazarin damarmakin da ake ba mata a bangaren shugabanci, kuma littafin zai taimaka wa illahirin matan Nijeriya.

Tun farko a jawabin ta, mawallafiyar kuma shugabar kungiyar matan sojoji Salamatu Yahaya, ta ce an rubuta littafin ne domin sake bude wa mata ido a bangaren shiga a dama da su a harkokin mulki da shugabanci.

Exit mobile version