Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Rashin Mai: PDP Ta Nemi Buhari Ya Sauka Daga Kujerar Ministan Man Fetur

Biyo bayan kalubalen da ake fuskanta tun bayan shigo da
gurbataccen man fetur, jam’iyyar PDP ta bukaci karamin
ministan man fetur Timipre Sylva ya yi murabus daga mukamin sa.

Jam’iyyar PDP, ta kuma nemi shugaba Buhari ya sauka daga
mukamin babban ministan man fetur ya mika wa kwararru su
rike kujerar.

Wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na
kasa Debo Ologunagba ya fitar, ta yi gargadin cewa jagorancin
jam’iyyar APC ne ke tursasa ‘yan Nijeriya su fito a kan tituna su
na zanga-zanga.

Sanarwar, ta ce zanga-zangar nuna adawa da gwamnati mai ci ta
na tasowa ne saboda ci-gaba da ganin cin hanci da rashawa da
rashin kula da jin dadin jama’a da gwamnatin shugaba Buhari ke
yi.

Exit mobile version