Daga ranar Talata, 14 ga watan Disamba gwamnatin Najeriya za ta dakatar da jirage daga ƙasashen Birtaniya da Kanada da Saudiyya da Argentina sauka a Najeriya a matsayin ramuwar gayya.
Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika ne ya sanar da matakin ranar Lahadi a Jihar Legas, yana mai cewa an ɗauki matakin ne da zimmar ramuwar gayya kan hana matafiya daga Najeriya shiga ƙasashen saboda nau’in korona na Omicron, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.
Ministan ya ƙara da cewa gwamnati za ta saka Birtaniya da Kanada da Saudiyya da Argentina cikin jerin ƙasashen da za ta haramta wa shiga ƙasar saboda annobar ta korona da kuma yaɗuwar Omicron.
Ministan ya ce kamar yadda suka yi mana, idan har ba za su ƙyale mutanen Najeriya su shiga ƙasashen su ba, to su wa jiragen su za su ɗauka idan suka shigo ƙasar mu.
Hadi Sirika, ya ce an gama tattaunawa cewa ba za a yarda ba kuma an ba da shawara a saka Birtaniya da Saudiyya da Kanada da Argentina cikin jerin dakatattun.