Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Peter Obi Ya Jibge Wa Kotu Rahotannin Manhajar Rumbun IREV Na INEC

Ɗan takarar zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Peter Obi, ya cigaba da damƙa wa kotu bayanan hujjojin da ya ke badawa domin kotu ta ƙwace nasarar da hukumar zabe ta ba Bola Tinubu na jam’iyyar APC ta ba shi ko kuma a sake sabon zaɓe.

A ranar Talatar da ta gabata ne, Peter Obi ya gabatar wa kotu rahotannin da hukumar zabe ta fitar dangane da Manhajar Rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe na IReV a Abuja.

Tun kafin zaɓe dai INEC ta yi alƙawarin cewa za ta watsa sakamakon zaɓe daga na’urar BVAS zuwa Manhajar Rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe ta yadda kowa zai shiga domin ya ga kwafin sakamakon zaɓen kowace rumfar zaɓe, amma ba ta yi hakan ba.

Wannan ya na daga cikin manyan dalilan da su ka sa Peter Obi ya garzaya kotu, inda ya yi zargin an yi maguɗi a zaɓen.

A ci-gaba da sauraren ƙarar, lauyan Peter Obi mai suna Peter Afoba, ya gabatar wa kotu rahoton Manhajar IReV daga jihohi biyar da su ka haɗa da Rivers da Akwa Ibom da Ekiti da Ogun da kuma Adamawa, sannan ya shaida wa kotun cewa dukkan rahotannin sai da hulkumar zaben ta tabbatar da cewa ita ce ta fitar da shi.

Exit mobile version