Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Jayayya Ta Kaure Bayan Lauyoyin Tinubu Sun Zargi Manhajar Amazon Da Haifar Da Matsala A Rumbun IREV

Lauyoyin Shugaba Bola Ahmad Tinubu, sun ya shaida wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa cewa  Rumbun Adana Bayanai na Amazon ba ya da tgabbas, domin ya na iya samun matsala.

Sai dai wani ƙwararren injinijya na Amazon ya ƙaryata lauyoyin shugaba Tinubu.

Atiku Abubakar na jamiyyar PPD da Peter Obi na jam’iyyar Labour dai  duk sun ƙalubalaci ƙin watsa sakamakon zaɓen, wanda su ka ce ba a watsa a rumbun IReV ba kamar yadda hukumar zabe ta yi alƙawari.

Jayayyar kuwa ta zo ne, mako guda bayan Peter Obi ya gabatar wa kotu tulin takardun sakamakon zaɓe dubu 18 daga rumbun IReV, wadanda ya ce ba su karantuwa.

Wani ƙwararren masanin manhaja da laƙanin sirrin komfuta ne ya bada shaidar cewa shafukan dubu 18 duk ba a iya ganin sakamakon zaɓen da ke cikin su.

Exit mobile version