Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

NSCDC Ta Kama Mahaifin Da Ya Yi Shekara Uku Yana Lalata Da ‘Yarsa A Jihar Kogi

Rundunar tsaro ta Civil Deffence a jihar Kogi, ta kama wani
magidanci dan shekaru 41 da ya rika yin fasikanci da ‘yar
cikin sa har na tsawon shekaru.

Kwamandan hukumar Ahmed Gandi ya sanar da haka, yayin da ya ke gabatar da mutumin ga manema labarai a helkwatar hukumar da ke Lokoja, inda ya ce rundunar ta kama mutumin ne bayan wata kungiya mai zaman kan ta ta kai kara a ofishin su.

Ahmed Gandi ya ce sakamakon binciken da su ka gudanar ya nuna cewa, mutumin ya fara yin fasikanci da ‘yar sa ne tun ta na da shekaru 16 daga shekara ta 2020 zuwa 2023.

Yarinyar ta bayyana wa manema labarai cewa, mahaifin ta ya fara fasikanci da ita ne tun da mahaifiyar su ta rabu da mahaifinsu, ta na mai cewa mahaifin ta ya yi mata ciki, da ya tabbata sai ya kai ta wani asibiti aka cire sannan ya cigaba da yin fasikanci da ita.

Da ya shiga hannun jami’an tsaro, mahaifin yarinyar ya tabbatar da aikata abin da ake tuhumar sa a kai, amma ya roki sassauci cewa sheɗan ne ya ingiza shi.

Exit mobile version