Jagoran kungiyar ‘yan aware ta IPOB Nnamdi Kanu, ya shigar da kara a wata kotun tarayya, ya na neman ta soke wani umarni da bangaren shari’a ya fitar cewa za a daina sauraren dukkan shari’un ta’addanci a bainar jama’a.
Nnamdi Kanu ya sanar da kotun ta hanyar lauyoyin sa cewa,
umarnin ya saba wa tsarin mulki da wasu dokokin Nijeriya, don
haka ya kamata ta soke shi.
A ranar 8 ga watan Afrilun nan ne, mai shari’a John Terhemba
Tsoho ya bada umarnin a daina sauraren shari’un da ke da alaka
da ta’addanci a bainar jama’a, domin kiyaye tsaron duk wadanda
ke da alaka da shari’ar.
Alkalin, ya kuma hana ‘yan jarida halartar zaman kotunan da ke
sauraren irin wadannan shari’u.
Baya ga alkalin da zai saurari shari’ar, mutanen da aka amince
su shiga dakin shari’ar sun hada da wasu zababbun ma’aikatan
kotun da jami’an tsaro.

