Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Nasarorin Da Muka Samu a Harkar Tsaro Ya Zarce Na Lokacin Jonathan – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce ‘yan Nijeriya su na da mantuwa ne, amma nasarorin da ya samu a harkar tsaro sun zarce waɗanda aka samu a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabin a wani taron
jam’iyyar APC da ya gudana a Abuja

Sai dai ‘yan Nijeriya na ganin duk da nasarorin da gwamnatin
Buhari ta samu, a karkashin mulkin sa an fi fama da kashe-
kashen mutane fiye da a lokacin gwamnatocin baya.

A yankin Arewa Maso Yamma da ya haɗa da jihar Katsina, ‘yan
bindiga sun kashe mutane da dama, sannan sun yi garkuwa da
wasu, wadanda har yanzu su na tsare a hannun su.

Jihohin Kaduna da Neja da Zamfara da Sokoto da Kebbi duk su
na fama da hare-haren ‘yan bindiga babu ƙakkautawa a
karkashin gwamnatin shugaba Buhari.

Exit mobile version