Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya yi ta maganganu a lokacin da ya ji a jikin sa cewa wasu mutane sun yi ma shi taron dangi sakamakon neman tikitin takarar shugaban kasa da ya ke yi.
Zancen Tinubu dai ya mamaye kafofin yada labarun Nijeriya gabanin zaben fidda dan takarar shugaban kasa, lokacin da ya fito ya na cewa shi ya fiddo shugaba Buhari daga murabus da ya yi a siyasar Nijeriya, tare da ikirarin cewa shi ya zabi Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban kasa.
Da ya ke jawabi yayin da ya kai ziyara fadar Oba na Lagos, Tinubu ya ce har sai da aka kai lokacin da ya ji komai ya gundure shi, ya na mai cewa babu wani dan asalin jihar Legas da ya taba samun damar zama shugaban kasa, duk kuwa da gudummawar da jihar ta bada wajen hadin kan Nijeriya.
Bola Tinubu dai ya samu galaba a kan a kan ‘yn takara 13 da su ka fito neman jam’iyyar APC ta tsaida su takarar shugabancin Nijeriya’ a wajen babban taron jam’iyyar da ya gudana a Abuja.

