Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Muric Ta Bukaci Tinubu Ya Ba Musulmai Mukaman Minista Fiye Da Kiristoci

Kungiyar kare hakkin Musulmai ta Nijeriya MURIC, ta bukaci zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba musulmai mukaman ministoci fiye da Kiristoci idan aka rantsar da shi.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya fitar, ya ce gwamnatoci da dama sun maida Musulmai tamkar saniyar ware a rabon mukaman gwamnati.

Ya ce akwai jihohi a shiyyoyin da musulmai su ka fi rinjaye musamman shiyyoyi masu jihohi shida, don haka ya kamata a ba Musulmai ministoci hudu sannan Kiristoci su dauki guda biyu domin samun daidaito.

Farfesa Ishaq Akintola, ya ba da misalan da jihohin Taraba da Adamawa da Bauchi a yankin Arewa maso Gabas, sai kuma jihohin Nasarawa Kogi da Neja a yankin Arewa taTsakiya, da kuma Oyo da Osun da Ogun da Lagos a Kudu maso Yamma da kuma jihar Kaduna a yankin Arewa maso Yamma.

Kungiyar, ta bayyana yadda gwamnatoci da dama su ka nuna wa Musulmai wariya duk da rinjayen da su ke da shi a wadannan yankunan, inda ta ce a jihohin Borno da Katsina da Sokoto kadai ne ake kula da hakkin Musulmai a lamurran gwamnati.

Exit mobile version