Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Mika Wuya: Wani Jigon Kungiyar Boko Haram Ya Hannanta Kansa Ga Sojoji A Jihar Borno

Wani babban shugaban kungiyar Boko Haram, wanda ake kira Amir Adamu Rugu rugu, tare da iyalansa sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Jihar Borno.

Amir Adamu wanda babban kwamandan kungiyar ne ya mika wuya ne ga sojojin rundunar Operation Hadin Kai a ranar Alhamis din nan a yankin Gwaza.

Wani babban jami’in tsaro ne dai ya tabbatar da cewa Amir Adamu ya mika wuya ne tare da matansa uku da ’ya’yansa ga dakarun Runduna ta 26 a garin Gwoza.

Bayanai sunce Amir Adamu ya yi kaurin suna wurin kai munanan hare-hare a kan sojoji da mazauna yankunan Dutsen Mandara da Dajin Sambisa da kuma Gwoza.

Mika wuyan nasa za zuwa ne bayan wasu shugabanni da mayakan Boko Haram tare da iyalansu mutum 1,081 suka mika wuya ga sojoji a Jihar Borno, bayan rikicin cikin gida da ya dabaibaye kungiyar bayan mutuwar Abubakar Shekau.

Hukumomin sojin Najeriya sun ce mayakan Boko Haram din na tururuwar mika wuya sakamakon luguden wuta da jiragen yaki keyi ne a maboyarsu.

Sojojin sun kuma ce rikicin shugabanci da yunwa da rashin lafiya da kunci da mayakan kungiyar suke fuskanta na daga cikin abubuwan da ke sa wasunsu barin kungiyar.

Exit mobile version