Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Mbappe Ya Fara Da Lashe Kofin UEFA Super Cup A Real Madrid

mixcollage 14 aug 2024 10 26 pm 2347

mixcollage 14 aug 2024 10 26 pm 2347

Real Madrid ta lashe kofin UEFA Super Cup na 2024/25, bayan da ta doke Atalanta da ci 2-0 a jiya Laraba a wasan da suka kara a birnin Warsaw a Poland.

Ƙungiyoyin sun tashi ba ci a minti 45 na farko, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Real ta fara cin ƙwallo ta hannun Federico Valverde, sannan Kylian Mbappe ya kara na biyu.

Wasan buɗe labulen gasar zakarun kungiyiyin Turai da aka yi kenan tsakanin Real mai kofin Champions League na bara da Atalanta mai kofin Europa League a kakar da ta wuce.

Real Madrid ta ɗauki Kylian Mbappe a bana daga Paris St Germain, domin kara karfin ƙungiyar, wanda shi ne na biyu a baya-bayan nan da ya ci ƙwallo a ƙungiyar a was an sa na farko.

Jude Bellingham ya yi wannan bajintar a Real Madrid a wasan La Liga da Athletic Club a Agustan 2023.

Kawo yanzu Mbappe ya ci ƙwallo bakwai a wasan karshe da ya haɗa da ɗaya a Coupe de France a 2021 da ɗaya a UEFA Nations League a 2021 da uku a wasan karshe

a gasar kofin duniya a Qatar a 2022 da ɗaya a Trophée des Champions a 2021 Paris St Germain da ɗaya a Uefa Super Cup a 2024.

Exit mobile version