Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Mayakan Ruwan Nijeriya Sun Toshe Hanyoyin Fasa Kwauri Da Satar Gurbataccen Mai

Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta Operation Dakatar Da Barawo, ta yi nasarar hana Nijeriya tafka asarar akalla Naira miliyan dubu biyu.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mayakan ruwan Nijeriya Navy Commodore Ayo Voughan ya raba wa manema labarai, yace jirgin mayakan ruwan ya kai wani farmaki, inda ya rugurguza haramtattun wuraren tace man fetur guda goma sha uku, da manyan Randunan adana mai guda shida da kuma karin
wasu manyan tankokin ajiye man guda biyu a jihar Rivers.

Wani jirgin ruwan sojin ya kuma kara lalata wani haramtaccen wurin tace man a birnin Warri na jihar Delta.

Rundunar ta hada jimillar alkaluman da ke nuna ta hana Nijeriya tafka asarar kimanin Naira miliyan dubu da miliyan dari tara da dubu dari biyar da dubu ashirin da shida da dari shida ta hanyar satar gurbataccen man.

Idan dai ba a manta ba, tun lokacin da ya karbi jagorancin rundunar sojin ruwan Nijeriya, Vice Admiral Auwal Zubairu Gambo ya sha alwashin dakatar da sata da safarar gurbataccen mai da kuma fashin teku.

Exit mobile version