Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Matatar Dangote Ta Sake Karya Farashin Dizal Da Man Jirgi

AIT IMAGES 4 10

AIT IMAGES 4 10

Matatar man Dangote ta sanar da sake rage farashin man dizal
da na man jirgi a kokarin saukaka farashinsa a sassan kasar
na.


Wannan na zuwa ne kasa da mako biyu bayan karya farashin farko da matatar tayi karkashin jagorancin shugaban kamfanin Aliko Dangote.

Sanarwar da matatar ta fitar, ta bayyana cewa daga yanzu za ta rika sayar da kowace litar man dizal a kan farashin Naira 940 sai kuma litar man jirgi akan farashin Naira 980.


Sanarwar ta bayyana cewa ragin farashin zai shafi masu cinikayyar da ke sayen litar man dizal miliyan biyar zuwa sama ne, yayin da abokan cinikayyar da za su sayi lita miliyan daya zuwa sama za su samu man dizal a kan farashin Naira 970.

Ragin farashin nazuwa ne yayin da ‘yan Nijeriya ke murna kan matakin farko na rage farashin man dizal ta yi daga Naira 1,200 zuwa 1,000.

Exit mobile version