Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta haramta gudanar da kowane nau’i na zanga-zanga a cikin birnin Abuja don tabbatar zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya DCP Frank Mba, ya ce shugaban ‘yan sandan Nijeriya Muhammadu Adamu, ya sa dokar haramta duk wani nau’i na yin zanga-zanga a cikin birnin Abuja.
Haka kuma, rundunar ta gargadi duk masu nufin yin wata zanga-zanga su kaurace wa wasu muhimman yankuna da gine-ginen gwamnatin tarayya musamman a yankunan da ke da nasaba da tsaron kasa.
Duk
da masaniyar ta a kan hakkin dan Adam na bayyana ra’ayi kamar yadda kundin
tsarin mulki ya tanada, rundunar ‘yan sandan ta ce, tsarin ya na iya sauyawa a
kowane lokaci musamman yayin da bada kariya.
�