Rundunar ‘yan sanda ta birnin tarayya, ta ce ta kama wasu kayan hada abubuwan fashewa a Abuja, ta na mai cewa jami’an ta sun kama kayan ne a tashar motar Baba-Nagode da ke unguwar Nyanya a wajen birnin Abuja.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Anjuguri Manzah ya sanya wa hannu, ta ce an kama mutane hudu da ake zargi da safarar kayan ba bisa ka’ida ba.
Ya ce mutanen da aka kama sun hada da wani Hamisu Abah da Suleiman Hammeed da Onuh Sunday da kuma Agwan Bulus.
Manzah ya cigaba da cewa, tuni an kaddamar da bincike a kan lamarin, yana mai bada tabbacin cewa akwai tsaro sosai a birnin Abuja. : 1596