Rundunar ‘yan Sanda ta birnin tarayya Abuja, ta ce sabanin jita-jitar da ake yadawa a kafofin yada labarai, masu garkuwa da mutane ba su yi wa birnin Abuja kawanya ba.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda ta birnin tarayya Abuja Anjuguri Manzah ya fitar, ya ba jama’a tabbacin cewa birnin Abuja ya na cikin kwanciyar hankali da tsaro, kuma cewa rundunar ‘yan sanda ta inganta dabarun ta na yaki da laifuffuka don tabbatar da tsaron rayuka da kadarorin jama’a.
Ya ce ya dace a bayyana wa al’umma cewa, rundunar ta yi nasara wajen kubutar da malamin jami’ar ‘Baze’ da aka yi garkuwa da shi ranar 8 ga watan Satumba na shekara ta 2019.
Kakakin rundunar ya kara da cewa, har ila yau su na son sanar da jama’a cewa sun soma gudanar cikakken bincike a kan lamarin, don ganin ta kubutar da wanda lamarin ta rutsa da shi.