Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Masu Zanga-Zanga Sun Kwashe Takardun Da Ake Tuhumar Ganduje

Abba Kabir Yusuf Governor Kano State

Abba Kabir Yusuf Governor Kano State

Gwamnatin jihar Kano ta zargi masu zanga-zangar da suka far wa babbar kotun jihar da kwashe takardun da ake tuhumar tsohon gwamnan jihar Ganduje kan cin hanci .

Cikin wata sanarwa da ya fitar, mai Magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusu, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya kwatanta al’amarin a matsayin abin takaici.

Gwamnatin jihar Kano ta shigar da karar tuhumar tsohon gwamna Ganduje da iyalan sa da wasu mukarraban sa ne kan zargin karkata akalar dukiyar jihar ta Kano.

Kalaman gwamnatin ta jihar Kanon na zuwa ne bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara harabar kotun a ranar Laraba,

domin ganewa kan sa yadda masu zanga-zangar suka lalata ginin kotun a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a ‘yan kwanakin da suka gabata.

Exit mobile version