Cibiyar Dakile Cututtuka ta Najeriya NCDC, ta ce an samu karin mutum 6 da suka kamu da cutar ta COVID-19 a daren Litinin.
Karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus din sun hada da mutum 2 a jihar Kwara, 2 a Jihar Edo, 1 a Jihar Ribas da kuma mutum 1 a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Cibiyar ta ce kawo yanzu mutum 238 ne suka kamu da cutar a Najeriya.
Daga cikinsu an sallami mutum 35 da suka warke daga asibiti, wasu mutum 5 sun mutu.
Hakan ke nuna zuwa yanzu mutum 198 ke kwance a cibiyoyin killace masu cutar COVID-19 a fadin Najeriya.
Adadin masu cutar COVID-19 a jihohin da ke fadin Najeriya sun hada da:
Legas – 120
Abuja – 48
Osun – 20
Oyo – 9
Edo – 11
Bauchi – 6
Akwa Ibom – 5
Kaduna – 5
Ogun – 4
Enugu – 2
Ekiti – 2
Rivers – 2
Benue – 1
Ondo – 1
Kwara – 2