Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Majalisar Najeriya Ta Amince Da Dokar Hukunta Masu Lalata Da Ɗalibai

Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar da za ta haramta tare da hukunta duk malamin da aka samu da laifin cin zarafi ko fasikanci da ɗalibai a kwalejoji da jami’o’in Nijeriya.

Tun a shekarata 2020, Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin, amma ya na ƙunshe da tanade-tanade daban-daban.

Shugaban kwamatin kula da harkokin shari’a na Majalisar Dattawa Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce taron gamayyar ‘yan majalisar ya haɗa kan tanade-tanaden biyu kafin ya gabatar da rahoton sa a zauren Majalisar.

Daga cikin tanadin dokar, akwai matakan daƙile yunƙurin aikata fasikanci da cin zarafi na jinsi a dukkan matakin karatun gaba da firamare a Nijeriya.

Mataki na gaba shi ne miƙa kundin dokar ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sanya mata hannu kafin ta zama doka.

Exit mobile version