Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya ce Majalisar Dokoki ta tarayya ta gamsu da ayyuka da matakan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka.
Sanata Akpabio ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya ce majalisar za ta haɗa hannu da bangaren zartarwa domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.
Ya ce Shugaban ƙasa ya riga ya fara ayyuka, kawai ya na buƙatar goyon bayan su ne domin ci-gaban ayyukan ƙasa, don haka za su bada shawarar ga abin da su ka gani ya zuwa yanzu.
Godswill Akpabio, ya ce Kasuwar hannayen jari ta na ƙaruwa kuma mutane da yawa sun yi matuƙar farin ciki da matakan da Tinubu ya ɗauka zuwa yanzu, don haka akwai sabon fata ba kawai ta fuskar tattalin arziki ba, amma ta fuskar zaman lafiyar ƙasa hakan zai shafi dukkan ɓangarorin rayuwa ciki har da tsaro.

